Za a raba jadawalin FA ranar Litinin

Bradford City Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana hasashen cewa Arsenal za ta iya kare kambunta a gasar

Ranar Litinin ne za a raba jaddawalin ci gaba da wasannin zagaye na biyar a gasar cin kofin kalubale na Ingila da ake kira FA.

Kulob din Bradford City wanda ya yi waje da Chelsea, yana daga cikin kungiyoyin da ke fatan taka rawar gani a gasar.

Haka ita ma Middlesbrough wacce ta fitar da Manchester City daga gasar tana daga cikin masu jiran tsammanin kulob din da za a hada su karawa.

Za a fitar da jaddawalin wasannin zagaye na biyar ne da karfe 19:00 agogon GMT, a inda Gary Lineker ne zai zamo babban bako.

Kulob din Cambridge City wanda ya tashi wasa da Manchester United babu ci, shi ne karamin kulob daga cikin kungiyoyi 21 da suka rage a gasar.