Sampdoriya ta kammala binciken lafiyar Eto'o

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Samuel Eto
Image caption Samuel Eto ya koma Everton ne bayan da kwantiraginsa ya kare da Chelsea

Dan kwallon Everton Samuel Eto'o na daf da koma wa taka leda kungiyar Sampdoriya ta Italiya, bayan da likitocin kungiyar suka duba lafiyarsa.

Dan wasan, mai shekaru 33, ya saka hotonsa tare da likitan kungiyar Sampdoria a shafinsa na Twitter, a inda ya ce an kammala duba lafiyarsa, kuma a shirye yake ya fuskanci sabon kalubale.

Eto'o ya koma Everton ne a watan Augustan 2014, a inda ya ci kwallaye hudu daga cikin wasannin da ya buga wa kulob din a bana.

Ranar 21 ga watan Janairu, kocin Everton Roberto Martinez ya karyata jita-jitar cewar dan wasan yana daf da koma wa Sampdoria.