Watakila CAF ta sauya filin karawa da Eq. Guinea

Afcon 2015
Image caption Equatorial Guinea za ta buga wasan gaba a ranar Asabar

Sakamakon kaiwa wasan daf da na kusa da karshe da Equatorial Guinea ta yi a gasar kofin Afirka da take karbar bakunci, zai sa CAF ta sauya filin wasan da za su fafata.

Equatorial Guinea ta samu kai wa wasan gaba ne bayan da ta doke makwabciyarta Gabon da ci 2-0 ranar Lahadi, ta kuma kare a mataki na biyu a rukunin farkon.

Hakan yasa mai masaukin bakin za ta kara da tawagar da ta zamo ta biyu a rukuni na biyun a filin wasa na Ebibeyin ranar Asabar.

Sai dai kuma ana fargabar cewa filin wasa na Ebibeyin wanda yake cin 'yan kallo 5,000 ba zai iya daukar 'yan kallon da za su bukaci ganin wasan ba.

Watakila mahukuntan gasar su maida wasan Bata, filin wasan da ya fi daukar 'yan kallo a kasar, kuma anan ne suka fara buga wasanninsu.