Van Persie ba shi da tabbas a United

Robin van Persie Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manchester United tana matsayi na hudu a teburin Premier

Dan wasan Manchester, United Robin van Persie, ya ce ba shi da tabbas idan Manchester United za ta tsawaita kwantiraginsa.

Kwantiragin Van Persie da United wanda ya koma kungiyar daga Arsenal kan kudi fam miliyan 24, zai kare ne a karshen kakar wasan 2016.

Dan kwallon, mai shekaru 31, ya kara da cewar ba shi da wuka da nama a hannunsa, bai sani ba idan zai ci gaba da wasa a United nan gaba.

Haka kuma ya ce yanzu kam baya cin kwallaye da yawa kamar yadda ya yi a kakar wasan bara.

Van Persie ya ci kwallaye takwas a wasanni 21 da ya buga a bana, wanda a kakar wasanni biyu da suka wuce ya ci kwallaye 30 a wasanni 18 da ya buga.