Newcastle ta nada Carver kociyanta

John Carver Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle tana matsayi na 11 a teburin Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta sanar da nada John Carver a matsayin sabon kociyanta har zuwa karshen kakar wasannin bana.

Kocin wanda ya yi mataimakin Alan Pardew a newcastle, zai jagoranci kungiyar ta kammala sauran wasanni 16 da suka rage a gasar Premier.

Mahukuntan kungiyar sun ce sai bayan an kammala gasar Premier ta bana ne za su duba idan ya kamata ya ci gaba da rike aikin ko kuma su musanya shi.

Tun lokacin da Carver ya karbi ragamar jagorancin kungiyar a matsayin rikon kwarya, ya yi rashin nasara a wasanni uku da yin canjaras a wasa daya.

Tun a farkon watannan ne Alan Pardew ya bar Newcastle don radin kansa, inda ya koma Crystal Palace.