Diafro: Giraisse ya kalubalanci West Ham

Kociyan kungiyar kwallon kafar Senegal, Alain Giresse, ya kalubalanci West Ham saboda wasan da dan wasan kasar ta Senegal, Diafro Sakho ya buga wa kulob din.

Sakho, mai shekaru 25, ya janye daga jerin 'yan wasan da zai yi wa kasar yayin gasar cin kofin nahiyar Afirka a farkon wannan watan sakamakon ciwon baya da yake fama da shi.

Amma sai ga shi an gano dan wasan yana taka wa kulob din West Ham leda ranar Lahadi.

Duk da cewa Sakho ya shiga wasan ne a minti na 57, ya samu nasarar zura kwallo daya a ragar Bristol City .

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kalubalanci kocin West Ham, Sam Allardyce

Al'amarin dai ya bai wa Alaine Giresse mamaki, ya kuma ce "West Ham ya bata harkar wasan kwallon kafa".