Fletcher zai bar Manchester Utd a kyauta

Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Darren Fletcher zai bar Manchester United

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Darren Fletcher, zai bar kulob din zuwa wata kungiyar wasan a kan tsarin musayar 'yan wasa.

Dan wasan, mai shekaru 30, wanda dan asalin Scotland ne, kuma ya buga wasanni guda 342 a kungiyar Manchester, duk da cewa ya buga wasanni biyar ne kawai a lokacin shugabancin Louis van Gaal.

Ana hasashen cewa Fletcher zai koma West Ham ko kuma West Brom idan kwantaraginsa ya kare daga Manchester a lokacin bazara.

Fletcher dai ya dade a Old Trafford, domin kuwa ya shiga kulob din ne tun yana dan makaranta.

Ya taimaka wa kulob din wajen zama zakara gasar Premier sau biyar.

Kociyan West Ham, Sam Allardyce, ya tabbatar da sha'awar da yake da ita ta rattaba hannu wajen karbar aron Fletcher.