Costa bai yi wa Emre keta ba - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Diego Costa da yin mugunta

Kociyan na Liverpool, Jose Mourinho ya karyata zargin cewa Diego Costa ya yi wa Emren Can keta a lokacin wasan kusa da-na-karshe na cin kofin Ingila da suka kara da Chelsea.

Costa dai ya taka Emre ne da Martin Skrtel a karin lokaci na tantance gwani, kafin daga bisani Chelsea ta jefa kwallo daya tilo, a ragar Liverpool.

Mourinho ya ce abin da Costa ya yi "tsautsayi ne" domin "hankalinsa yana kan kwallo ne".

Chelsea ya doke Liverpool da ci 1-0 a fafatawar.

Yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Ingila tana sauraron hukuncin da alkalin wasa, Michael Oliver, zai yanke kan al'amarin, kafin hukumar ta dauki matakin da ya dace.