Tennis: Djokovic ya lallasa Milos Raonic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Djokovic zai kara da Stan Wawrinka

Zakaran wasan Tennis har karo hudu,Novak Djokovic ya hana Milos Raonic zuwa wasan kusa da-na-karshe a gasar wasan Tennis ta Australian Open, a Melbourne.

Djokovic dai ya lallasa Milos ne da ci bakwai da shida da kuma shida da hudu ya kuma kara masa da ci shida da biyu.

Hakan dai ya ba wa, dan wasan mai shekaru 27 cancantar zuwa wasan kusa da-na-karshe karo na 25 kenan.

Kuma sai kara da dan wasa mai rike da kofi har sau uku, Stan Wawrinka.