FIFA: Luis Figo zai kalubalanci Blatter

Image caption Tsohon dan kwallon Real Madrid, Luis Figo

Tsohon dan kwallon kasar Portugal, Luis Figo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin FIFA domin kalubalantar Sepp Blatter.

Figo wanda tsohon gwarzon dan kwallon duniya ne, ya ce ya yanke shawarar yin takara ne saboda yadda yake son kwallon kafa kuma yana so ne ya maidoda martabar Fifa a idon duniya.

A cewarsa yana da goyon bayan kungiyoyin kwallon kafa na kasashe biyar, abin da ya ba shi damar shiga takarar a fafata da shi.

Luis Figo mai shekaru 42, ya taka leda tare da Real Madrid da Barcelona da kuma Inter Milan.

Sauran wadanda ke hammaya da Sepp Blatter a zaben da za a gudanar a watan Mayu sun hada da Yarima Ali Bin Al-Hussein na Jordan da kuma tsohon dan wasan Faransa, David Ginola.