Ba zan koma Man Utd ba – Bale

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale ya ce yana jin dadin zamansa a Real Madrid

Dan wasan gaba na Real Madrid, Gareth Bale, ya tabbatar da cewa ba zai bar kulob din zuwa Manchester United ba.

An yi ta rade radin cewa Bale -- mai shekaru 25 -- yana son komawa Manchester United, yayin da golan United, David De Gea ke son komawa Madrid.

Sai dai Bale ya shaida wa gidan rediyon Cadena SER cewa "ba zan koma Manchester United. Ina jin dadin zama na a nan, domin kuwa muna lashe gasa da da dama. Ina son ci gaba da zama a Real Madrid."

Bale ya koma Real a kan kudi £85m a watan Satumba na 2013, kuma da shi aka lashe kofin Zakarun Turai a kakar wasa ta bara.