Costa zai kalubalanci hukuncin FA

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Costa ba zai buga wasan da Chelsea zai yi da Manchester City ba idan aka same shi da laifi

Dan wasan Chelsea Diego Costa zai kalubalanci hukumar kwallon kafar Ingila.

Hukumar ta tuhumi dan wasan kasar Spaniyan ne ranar Laraba bisa rashin da'a saboda ya taka dan wasan Liverpool, Emre Can.

Haka kuma ana tuhumar da taka dan wasan baya na Liverpool, Martin Skrtel, a kusa da ragar kulob din kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan da suka yi.

A ranar Juma'a ne kwamitin da'a zai zauna domin yanke hukunci na yiwuwar dakatar da Costa daga buga wadansu wasanni.

Idan aka samu dan wasan da laifi, hukuncin farko da zai fuskanta shi ne na hana shi buga wasan da kulob din Chelsea zai yi da Manchester City ranar Asabar.