Boko Haram: Ban ki-moon ya yi maraba da sojin hadin gwiwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ban ki-moon, Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Babban sakataren majalisar Dinkin-duniya, Ban ki-moon ya yi maraba da shirin tarayyar Afirka, wato AU na kafa rundunar sojin hadin gwiwa, a Afirka ta yamma domin yakar Boko Haram.

Ban ki-moon wanda ya bayyana hakan ranar Asabar ya ce " ina maraba da kudirin tarayyar Afirka da kasashen Afirka ta yamma na kafa rundunar sojin hadin gwiwa domin yakar Boko Haram".

Ya kara da cewa " Boko Haram sun aika ta munanan laifukan yaki, ya kamata a magance wannan matsalar ta fuskar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka ta yamma da sauran kasashen duniya".

Kasashe biyar ne dai da suka hada da Najeriya da Kamaru da Chadi da Niger da kuma Benin za su kafa rundunar sojin hadin gwiwar.

Rundunar dai idan har an kafa ta, za ta kunshi sojoji 7,500.