Ina son ci gaba da zama a Swansea —Shelvey

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kociyan kulob din ya ce ba zai ci gaba da amince wa da gandar Jonjo ba

Dan wasan Swansea City da Ingila, Jonjo Shelvey, ya ce yana son ci gaba da taka leda a kulob din har sai ya zama zakara.

Kociyan kulob din, Garry Monk, ya gargadi dan wasan mai shekaru 22 a watan Disamba cewa ba zai amince da gandar da yake yi ba.

Shelvey ya zura wata kwallo mai armashi a wasan da suka doke Southampton da ci 1-0 a fitowarsa ta farko a gasar Premier tun bayan karawar da suka sha kashi a hannun Liverpoool da 4-1 ranar 29 ga watan Disamba.

Dan wasan ya ce, "Ina son ci gaba da taka leda a nan domin nuna kwazo na. Wannan shi ne batun da na fi bai wa muhimmanci a yanzu ."

Shelvey ya kara da cewa zai ci gaba da gwada bajintarsa a filin wasa da kuma lokacin atisaye.