Kofin Africa: An dakatar da wasu alkalan wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An ci tarar wani dan Tunisia $50,000

An dakatar da wasu alkalan wasa da suka jagoranci wasa tsakanin Tunisia da Equatorial Guinea a gasar cin Kofin Africa har tsawon watanni shida.

Hukumar kwallon Afrika CAF ce ta dakatar da su ne sakamakon hukuncin da suka dauka na bai wa mai masaukin baki Equatorial Guinea bugun fenariti ana gab da tashi daga wasa.

An ci tarar wani dan kasar Tunisia, Rajindraparsad Seechurn $50,000 saboda aikata ba daidai ba.

CAF kuma ta bukacin kasar Tunisia ta nemi afuwa saboda zargin da Tunisiar ta yi na cewa an nuna son kai.

Kazalika an bukaci Tunisia ta biya kudin gyaran abubuwa da aka lalata a filin wasa na Bata bayan kammala wasan.