Carlisle ya yi yunkurin kashe kansa

Image caption Clarke Carlisle ya ce yana cikin kuncin rayuwa.

Tsohon dan wasan Burnley, Clarke Carlisle, ya ce ya so ya kashe kansa ne a lokacin da wata babbar mota ta kade shi a watan Disamba.

A wata hira da ya yi da jaridar Sun ta Ingila, Carlisle ya ce an bar shi cikin kunci bayan kammala rayuwarsa ta kwallon kafa, yana mai cewa ba shi da kudi.

An sammali tsohon dan wasan, mai shekaru 35, daga asibiti ranar 30 ga watan Janairu, makonni shida bayan motar ta kade shi a yankin Yorkshire.

Ya ce, "wannan shi ne lokacin da na fi fuskantar kunci a rayuwa ta."

Carlisle shi ne shugaban kungiyar kwararrun 'yan wasa daga 2010 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama a cikin kwamitin zartarwa na kungiyar .

An haife shi ne a Preston, kuma ya fara taka leda a kulob din Blackpool, inda ya buga wasanni fiye da 500 a kungiyoyin kwallon kafa tara da ya taka wa leda cikin shekari 16, sannan ya yi ritaya a shekarar 2013.