Diafra Sakho: Fifa ta ci West Ham tarar £71,000

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fifa ta ce West Ham ta karya doka

Hukumar kwallon kafar duniya, Fifa ta ci kulob din West Ham tarar £71,000 bayan an same shi da laifin yin amfani da dan wasan Senegal Diafra Sakho ba bisa ka'ida ba.

Sakho, mai shekaru 25, ya janye daga bugawa kasarsa ta Senegal a gasar cin Kofin nahiyar Africa saboda ciwon bayan da yake fama da shi.

Sai dai kwanaki 18 bayan ya ce yana ciwon baya, ya taka leda a West Ham, har ma ya zura kwallo a fafatawar da kulob din ya doke Bristol City 1-0 a Gasar cin Kofin Ingila.

Dokar Fifa ta bayyana cewa dan wasa ba zai bugawa kulob din sa kwallo ba idan dai kasarsa ta bukace shi domin ya taka mata leda.