An yi yamutsi a wasan Ghana da Eq. Guinea

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An fara yamutsin ne bayan Ghana ta doke Equatoril Guinea 3-0

An yi yamutsi a Malabo, babban birnin Equatorial Guinea lokacin da Ghana ta doke kasar a wasan kusa da na karshe na cin Kofin nahiyar Africa .

Lamarin dai ya sa an dakatar da wasan tsawon mintuna talatin.

Magoya bayan Ghana sun tsere sakamakon duwatsun da aka yi ta jifansu da su minuta 82 da fara wasan.

An yi ta jifansu da kwalabe, yayin da 'yan sanda ke kokarin kubutar da su, sannan kuma sai da aka sa jirage masu saukar ungulu suka rika shawagi a saman filin wasan domin firgita masu tayar da rikici.

An ci gaba da wasa, kuma a lokacin ne Ghana ta zura kwallo inda aka tashi 3-0, lamarin da ya ba ta damar kai wa wasan karshe, wanda za ta fafata da Ivory Coast ranar Lahadi.