Leicester: ba mu kori Nigel Pearson ba

Image caption Nigel Pearson har yanzu shi ne shugaban Leicester

kungiyar wasa ta Leicester ta musanta rahotanni da ke cewa ta kori manajan kulob din, Nigel Pearson.

Rahotanni dai sun nuna cewa kulob din ya kori Nigel, mai shekaru 51, bayan kungiyar Crystal Palace ta lallasa kulob din da ci daya da nema, a ranar Asabar.

Sai dai wata sanarwa da aka fitar bayan karfe 22:00 agogon GMT ranar Lahadi, ta nuna cewa Pearson ne shugaban Leicester.

Sanarwar ta ce " duk wani rahoto sabanin wannan to labarin kanzon kurege ne"