Za mu kwato kambunmu - Cristiano Ronaldo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristiano Ronaldo

Dan wasan kulob din Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya ce yana da yakinin cewa kulob din sa zai kwato kambun gasar La Liga, ta kasar Spaniya daga kungiyar Atletico Madrid.

Duk da cewa kulob din na Atletico Madrid ya lallasa Real Madrid da ci hudu da nema, har yanzu Real Madrid ce a saman teburin gasar La Liga.

Ronaldo ya ce "A tunanina, kulob dinmu yafi na Atletico kuma ya kamata mu nuna hakan a yayin wasa. Na yi yakinin cewa a karshe za mu samu nasarar zama zakara a La Liga."

Yanzu haka kulob din Barcelona ne na biyu, sannan Atletico Madrid ta kasance ta uku da maki hudu.