Sam Allardyce: Man Utd zari-ruga ta yi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Manajan kulob din West Ham, Sam Allardyce

Manajan kulob din West Ham, Sam Allardyce ya ce kungiyar Manchester United ta samu sakamako me kyau a kansu ne bayan 'yan wasanta sun koma yin zari-ruga.

Ya ce "A karshe, mun kasa yin wasan saboda dukan kwallo sama da 'yan wasan Manchester United suka rinka yi."

Ya kara da cewa "Sun ta yi wa kwallo dukan-kan-mai-uwa-dawabi, kuma daga karshe sun sami nasara."

Sai dai kuma shugaban kulob din na Manchester United, Louis van Gaal ya ce dole ce ta sanya kulob din buga irin wannan tamaular saboda yadda irin halin da suka shiga kafin zuwa hutun rabin lokaci.

An tashi kunen doki ne a wasan da aka fafata a filin Upton Park, kuma ya sa United ta ci gaba da kasancewa a matsayi na hudu a kan tebur, a yayinda West Ham ke mataki na takwas.