FA ba za ta hukunta Nigel Pearson ba

Image caption FA ba za ta hukunta Nigel Pearson ba

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ba za ta hukunta manajan kulob din Leicester, Nigel Pearson ba, sakamakon makure dan wasan kungiyar Crystal Palace, James McArthur, da ya yi, a wasan da kungiyoyin biyu suka kara ranar Asabar.

Hukumar ta FA ta yanke shawarar kin ladabtar da Nigel ne bayan da ta tuntubi shugabannin wasa wadanda suka shaida yadda al'amarin ya faru.

Sai dai kuma hukumar ta aike masa da wasika domin tunatar da shi irin halayyar da ya kamata ya nuna a matsayinsa na shugaba.

Nigel Pearson dai ya shake McArthur ne bayan da shi dan wasan ya tunkude shi.

Kulob din Crystal Palace dai ya lallasa na Leicester da ci daya da nema, a wasan.