Aston Villa ta kori kocinta Paul Lambert

Paul Lambert Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aston Villa tana matsayi na 18 a teburin Premier bana

Kungiyar Aston Villa ta kori kocinta Paul Lambert, bayan da ta koma matakin 'yan ukun karshen teburin Premier bana.

Villa ta sha kashi a hannun Hull City da ci 2-0 a gasar Premier ranar Talata, kuma wasa na 10 kenan da kungiyar ba ta ci wasa ba.

Kuma kwallaye 12 Villa ta ci a gasar bana, wanda hakan shi ne tarihin karancin zura kwallaye a raga a Premier daga cikin wasannin 25 da ta buga.

Kocin mai shekaru 45 ya fara aiki da kungiyar a shekarar 2012, ya kuma tsawaita kwantiraginsa zuwa Yunin 2018 ranar 17 ga watan Satumba.

An bai wa Scot Marshall da kuma Andy Marshall damar su jagoranci kulob din a matsayin rikon kwarya.