Balotelli ya ceto Liverpool daga hannun Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Balotelli ne ya ceto Liverpool daga hannun Tottenham

Kwallon farko da Mario Balotelli ya zura a gasar Premier ta bana ta bai wa Liverpool nasara a kan Tottenham a fafutikar da suke yi na zama daya daga cikin kulob hudu a saman tebirin gasar.

Kulob din Liverpool ne ke kan gaba da ci 2, sai dai Tottenham sun farke kafin a sanya Balotelli wanda ya maye gurbin Daniel Sturridgee mintuna bakwai kafin a tashi daga wasa.

Nan da nan Balotelli ya samu kwallo ya zura, lamarin da ya sa suka tashi da ci 3-2.

Koda yake Raheem Sterling bai taka leda ba saboda raunin da ya ji, amma Sturridge ya dawo bakin-daga a karon farko tun karawar da Liverpool suka tashi 3-0 a White Hart Lane ranar 31 ga watan Agusta.