Chelsea ta doke Everton da ci 1-0

Chelsea Everton Hakkin mallakar hoto mike hewit
Image caption Chelsea tana mataki na daya a teburi da maki 59

Chelsea ta samu nasara akan Everton da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 25 da suka fafata a filin wasa na Stamford Bridge.

William ne ya ci kwallon daf a tashi daga wasa, bayan da aka bai wa Gareth Bale jan kati a wasan.

Chelsea ta kai hare-hare da dama, a inda golan Everton Tim Howard ya hana kwallayen da Loic Remy da Nemanja Matic da Willian suka buga masa shiga raga.

Shi ma golan Chelsea Petr Cech ya hana kwallon da Romelu Lukaku ya buga masa shiga ragar.

Chelsea ta bai wa Manchester City wacce take mataki na biyu a tebrurin Premier tazarar maki bakwai tsakani.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

Chelsea 1 - 0 Everton Man Utd 3 - 1 Burnley Southampton 0 - 0 West Ham Stoke 1 - 4 Man City Crystal Palace 1 - 1 Newcastle West Brom 2 - 0 Swansea