Lambert ya san aikinsa na tangal-tangal

Lambert Out Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Aston Villa tana mataki na 18 a teburin Premier

Kociyan Aston Villa Paul Lambert ya ce ya kwan da sanin cewar magoya bayan kulob din na daf da yi masa bore.

Villa ta kasa cin wasanni goma da suka wuce a gasar Premier, kuma ta koma mataki na 18 a teburi bayan da Hull ta doke ta 2-0 ranar Talata.

Magoya bayan kulob din sun daga kyalle a wasan mai dauke da sakon 'A kori Lambert'.

Kociyan ya ce ya dade da sanin haka za ta faru a kansa tun tuni, amma yana iya kokarinsa ya ceto kulob din daga halin da ya shiga.

Ranar 17 ga watan Satumba ne Lambert mai shekaru 45 ya tsawaita kwantiraginsa da Villa wadda za ta kare cikin watan Yunin 2018.