Mococco ba ta amince da hukuncin CAF ba

CAF Logo
Image caption Morocco ta ce za ta bi hanyar da ta dace domin a rage mata hukuncin

Morocco ta yi watsi da hukuncin da CAF ta yanke mata, saboda kin karbar bakuncin gasar kofin Afirka na 2015 da ta yi..

CAF ta dakatar da Morocco daga shiga gasar kofin Afirka biyu masu zuwa, za ta biya tarar dala miliyan, sannan ta sake biyan Euro miliyan takwas kudin hasarar rashin karbar bakuncin gasar da ta yi.

Hukumar kwallon kafar Morocco ta ce ba ta amince da hukuncin da aka yanke mata ba, da kuma tararta da aka ci.

Morocco ta ki karbar bakuncin gasar kofin Afirka da aka kammala a Equatorial Guinea, saboda tsoron ka da akai mata cutar Ebola har gida.

Saboda hakan ne Morocco ta bukaci CAF ta dage wasannin zuwa shekarar 2016, lamarin da CAF ta ki amincewa da shi.