Wenger ya damu kan raunin da Ramsey ya ji

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Aaron Ramsey ya kasa taka kafarsa bayan jijiyoyinsa sun rike.

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya yi matukar nuna damuwa sakamako jin raunin da dan wasan tsakiya Aaron Ramsey ya yi a wasan da suka doke Leicester City 2-1.

An sanya Ramsey, mai shekaru 24, a cikin wasan ne mintuna 73 da fara wasa sai dai ya fara dingishi bayan jijiyoyin kafarsa sun rike.

Wenger ya ce, "Ya yi wuri ga Aaron ya fara dingishi, amma kuma abin da ya faru ke nan; nan take ya kasa taka kafarsa, kuma hakan alama ce ba mai karfafa gwiwa ba ."

Kazalika, an cire Alexis Sanchez daga wasan, koda yake Wenger yana sa rai dan wasan zai taka leda a karawar da za su yi da Middlesbrough a gasar cin Kofin FA ranar Lahadi.

Da ma dai tsohon dan wasan na Barcelona ya dawo ne bayan raunin da ya yi a kafadarsa.

Ramsey ya nuna gajiyawa lokacin da yake zaune yana jiran likitoci su zo domin dauke shi daga filin wasa.