Man United ya yi hasarar kudin shiga

Old Trafford Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption United tana mataki na uku a teburin Premier da maki 47

Kulob din Manchester United ya ce ya yi hasarar kudin shiga da ya kai kaso 12 cikin dari daga watanni shida zuwa karshen Disamba.

United ya yi rashin kudin shiga mai tsoka daga kamfanin Nike, sakamakon kasa shiga gasar kofin zakarun Turai da ya yi a bara.

Kulob din kuma ya yi hasarar kudin shiga wajen nuna wasanni a talabijin da shiga kallon wasa da ya kai sama da fam miliyan tara.

Sai dai United ya ce ya samu karin kudin shiga daga tallace - tallace da suka kai sama da Fam miliyan 35, da hakan ya rage masa hasara.