Woods zai dakata da buga kwallon golf

Tiger Woods Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da ya dauki kofi tun a shekarar 2008

Tiger Woods ya ce zai dan dakata daga shiga gasar golf zuwa wani lokaci, bayan da ya kasa dawo wa kan ganiyarsa.

Dan wasan ya ce zai dawo shiga gasar wasanni ne idan har ya samu atisayen da ya kamata a yi gumurzu tare da shi.

Woods wanda ya yi fice a wasan golf a duniya na fuskantar kalubalen wasan, kuma rabon da ya dauki kofi tun a shekarar 2008.

Ciwon bayan da yake fama da shi a shekaru da dama na daya daga cikin abubuwan da ke kawo masa tsaiko a wasan.

Haka kuma sau uku yana janye wa daga manyan wasanni tara a baya da hakan ya kawo masa koma baya a wasanninsa.