Carroll zai yi jinyar makonni hudu zuwa shida

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Carroll ya cika laulayi

Dan kwallon West Ham, Andy Carroll, zai yi jinyar akalla makonni hudu zuwa shida saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.

Carroll ya ji raunin ne a wasan da suka tashi babu ci tsakaninsu da Southampton.

Kocin West Ham Sam Allardyce ya ce, "Ya ji mummunan rauni a cikin tsokar da ke gwiwarsa."

Carroll mai shekaru 26 hakan nan ya ci ba da taka leda a wasa saboda West Ham ta riga ta gama canjinta a wasan.

Wasan West Ham na gaba shi ne tsakaninta da West Brom a wasan zagaye na biyar a gasar cin kofin FA.