Ingila za ta gayyaci Kane

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kane na haskakawa a Spurs

Kocin Ingila, Roy Hodgson, ya tabbatar da cewa dan kwallon Tottenham Harry Kane zai shiga cikin tawagarsa a watan gobe.

Ingila za ta buga wasanni a cikin watan Maris tsakaninta da Lithuania da kuma Italiya.

Hodgson ya bayyana dan wasan mai shekaru 21 a matsayin "wanda ke da duk abubuwan da ake bukata daga wajen dan wasan gaba."

Kane ya zura kwallaye 23 cikin wasanni 35 a kakar wasa ta bana.

"Yana da gurbi a cikin wannan tawagar," in ji Hodgson.

Ana sa ran kyaftin din Ingila, Wayne Rooney shi ma zai buga bangaren gaba a wasan duk da cewa a Manchester United yana buga tsakiya ne.