U17: Najeriya ta casa Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan shi ne karon farko da Nijar ke karbar bakuncin gasar matasan

Najeriya ta doke Nijar 2-0 a wasan cin kofin kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 17 wanda aka fara Lahadin nan a Yamai.

Gasar wadda Nijar din ke karbar bakuncinta ta kunshi kasashe takwas da ka raba su rukuni biyu.

Rukunin farko (Group A) ya kunshi Nijar da Najeriya da Guinea da kuma Zambia.

Rukuni na biyu kuma ya hada da Kamaru da Ivory Coast da Mali da Afrika ta Kudu.

A ranar 18 ga watan nan na Fabrairu Najeriya mai rike da kofin na duniya, za ta yi wasa na biyu da Guinea, sannan ta kara da Zambia ranar 21 ga watan na Fabrairu.

Duk kasashe hudu da suka kai wasan kusa da karshe na gasar a Nijar, za su cancanci zuwa gasar ta duniya da za a yi a kasar Chile, tsakanin 17 ga watan Nuwamba zuwa takwas ga Disamba na 2015.