Van Gaal : Sai Valdes ya dage ya yi wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau bakawai Victor Valdes yana zaman benci a wasannin Man United tun watan Janairu

Kociyan Manchester United Louis van Gaal, ya ce dole ne sai Victor Valdes ya nuna kansa cewa ya farfado sosai kafin ya sa shi a jerin 'yan wasan kungiyar na farko.

Golan dan kasar Spain wanda ya warke daga mummunan raunin da ya yi jiyya na guiwa, wasa daya ya buga wa kungiyar tun da ya shige ta a watan Janairu, shi ma na kananan 'yan wasanta.

Tsohon golan na Baecelona, mai shekaru 33, shi ne ke zaman ko-ta-kwana a bayan David De Gea mai shekaru 24.

Van Gaal, ya ce, idan ba ka wasa sama da shekara daya, dole ne sai ka jajirce ka fito da kanka a cikin kananan 'yan wasa kafin ka samu gurbi a cikin manyan 'yan wasa.

Bayan daukar golan na tsawon kwantiragin watanni 18, kociyan ya ce, ba wanda zai so ya ga an mayar da shi matsayi na biyu.

Kocin ya ce, dole ne ya yi wasa a karamar kungiyarmu kamar yadda Ashley Young yake yi da Micheal Carrick, abu ne da aka saba yi.

Valdes wanda ya dauki kofin Zakarun Turai uku da na La Liga shida, ya buga wa Man United wasan farko da kungiyarta ta 'yan kasa da shekara 21 ta doke Liverpool ranar 26 ga watan Janairu.