Kofin FA: Bradford na zaman jira

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bradford su ne kurar baya a tsakanin kungiyoyin da suka kai wannan mataki

Makasan maza a gasar cin kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, Bradford City na jiran sanin wadanda za su kara da su a wasan dab da na kusa da karshe ranar Litinin din nan.

Kungiyar ta League One ta biyo nasarar da ta samu a kan Chelsea ta ci 4-2 da buge Sunderland 2-0, ranar Lahadi.

Kociyan Ingila Roy Hodgson shi ne zai jagoranci hada jadawalin yadda kungiyoyin za su hadu kafin karawar Manchester United da Preston.

Hodgson zai samu tallafin Brian Finney dan tsohon zakaran dan wasan Preston, Sir Tom Finney.

Bradford City ita ce karamar kungiya a cikin kungiyoyi takwas da suka kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar ta kofin FA.

Kungiyoyin da suka kai matakin su ne; Liverpool da Arsenal da Aston Villa da West Bromwich Albion da Bradford City da Blackburn Rover da Reading.

Sai kuma Preston North End ko Manchester United.