Luiz: Ba zan yi murna ba idan na ci Chelsea

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zan mutunta Chelsea a karawarmu

Tsohon dan wasan Chelsea, David Luiz, wanda ya koma PSG, ya ce ba zai yi birede (murna) ba idan ya zura kwallo a ragar Chelsea a wasan da za su yi na Kofin Zakarun Turai ranar Talata.

David Luiz wanda ya taimaka wa Chelsea ta fitar da PSG a wasan dab da na kusa da karshe na gasar a bara, a bana yana tare da PSG din.

Dan wasan na Brazil, wanda ya koma PSG a kan fam miliyan 50, a bazarar da ta wuce, ya ce yana son ya yi nasara kamar yadda ya yi a shekarar da ta wuce, amma a wannan karan da PSG.

Luiz, ya ce, '' idan na jefa kwallo a ragar Chelsea ba zan yi biride ba (murna) domin in mutunta su, amma dai zan yi farin ciki.

Dan wasan ya dauki kofin Zakarun Turai da Chelsea a 2012 kuma ya taimaka musu suka dauki kofin Europa a 2013.

Kungiyar Paris St-Germain za ta fuskanci wasan na farko na zagayen 'yan 16 na kofin zakarun Turai da Chelsea tare da matsalar rashin 'yan wasa saboda rauni.

PSG wadda za ta karbi bakuncin Chelsea a karawar ta farko, ranar Talata, a Paris, za ta yi wasan ne ba tare da Yohan Cabaye da Marquinhos da Serge Aurier wadanda suka ji rauni a karshen mako yayin wasansu da Caen da suka tashi 2-2, shi ma Lucas na fama da rauni

Ita kuwa kungiyar Chelsea na tababar amfani da Mikel Obi ne saboda matsalar ciwon guiwa, yayin da shi kuma Oscar ya samu sauki kuma ake ganin kila ya buga wasan.