FA: Man United za ta kara da Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fellaini ke nan yana ci wa Man United kwallo ta biyu

Manchester United za ta hadu da Arsenal mai rike da kofi a wasan dab da na kusa da karshe na kofin FA bayan ta doke Preston da ci 3-1.

Dan wasan kungiyar ta Preston, S. Laird shi ne ya fara jefa kwallo a ragar man United a minti na 47.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne, a minti na 65, Ander Herrera ya rama wa United.

Can kuma a minti na 72 sai Fellaini ya kara ci wa United, kafin kuma Rooney ya samu fanareti, inda bai yi wata-wata ba ya sheka ta a raga.

A jadawalin wasan dab da na kusa da karshen wanda kocin Ingila Roy Hodgson ya hada, Liverpool za ta hadu da Blackburn Rovers.

Bradford City za ta kara da Reading, yayin da Aston Villa za ta kara da West Brom.