Fifa: Barca na iya sayen 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fifa ta hukunta Barcelona ne akan saba ka'idojin sayen matasan 'yan wasa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta tabbatar da cewa kungiyar Barcelona za ta iya sayen 'yan wasa matukar ba ta yi rijista ba kafin watan Janairu na 2016.

A watan Afrilu ne na 2014, Fifa ta haramta wa kungiyar sayen sabbin 'yan wasa bayan saba ka'idojinta na sayen 'yan wasa 'yan kasa da shekara 18.

A lokacin Fifa ta yi watsi da daukaka kara da kungiyar ta yi na haramcin a watan Agusta, amma kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya ta bai wa kungiyar damar sayen 'yan wasa kafin rufe kasuwar a bazara.

Bayan kotun ta duniya ta kuma yi watsi da daukaka karar kungiyar a kan hukuncin haramcin a watan Disamba, sai aka dauka Barca ba za ta sake sayen 'yan wasa ba a wannan shekara.

Wasu rahotanni na nuna cewa kungiyar ta Barcelona na harin sayen dan wasan Manchester United Juan Mata da na Porto Danilo.