Kofin FA: Arsenal za ta gwabza da Man U.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester U. ta sha kashi a hannun Arsenal a wasansu na karshe na cin Kofin FA

Kulob din da ke rike da Kofin FA, Arsenal, zai fafata da Manchester United a wasan quarter final ranar 7 ga watan Maris.

Kulob din United ya tsallake zuwa wasan quarter final ne bayan ya doke Preston North End da ci 3-1.

Marouane Fellaini, wanda ya ci wa Manchester United kwallo ta biyu a wasan da suka yi da Preston, ya ce yana shaukin ganin sun fafata da Arsenal.

Arsenal da United sun yi karawar karshe ne a kakar wasan FA ta shekarar 2004-05 a Cardiff, inda Arsenal din ta yi nasara a bugun fenareti da ci 5-4 bayan.

Tashar BBC One za ta watsa wasan, wanda za a yi a Old Trafford.