Kotu ta samu Tottenham da laifi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan bai san yana da ciwon zuciya ba

Alkalin wata babbar kotu ya samu Tottenham da saba ka'ida kan daukar wani matashin dan wasa da ya gamu da ciwon zuciya a wasansa na farko da kungiyar.

Dan wasan Radwan Hamed ya yanke jiki ya fadi a lokacin da kungiyar matasan 'yan wasan Tottenham ke wasa a Belgium a watan Agusta na 2006, abin da ya haddasa masa illa a kwakwalwarsa.

A lokacin tantance lafiyarsa kafin a dauke shi a kungiyar, an ga cewa yana da matsalar bugun zuciya, amma duk da haka aka dauke shi.

Mahaifin dan wasan, Raymond, ya dora alhakin ciwon da ya samu dan nasa na kwakwalwa a kan sakacin likitocin da suka tantance shi.

Alkalin kotun kuwa, Mr Justice Hickinbottom, ya yanke hukuncin cewa kungiyar Tottenham, tana da laifi kashi 70 cikin dari, yayin da likitan zuciya na hukumar kwallon Ingila, Dr Peter Mills, yake da laifi kashi 30 cikin dari.

A wata sanarwa da kungiyar ta Tottenham ta fitar ta ce ta yi nadama kan abin da ya faru.

Nan gaba ne kotun za ta zartar da diyyar da za a biya dan wasan, wadda ake ganin za ta iya kaiwa fam miliyan bakwai.