U17: Najeriya da Guiea sun yi 1-1

Hakkin mallakar hoto D
Image caption Kasashe hudu daga gasar za su wkilici Afrika a gasar ta duniya da za a yi a Chile

Najeriya da Guinea sun tashi 1-1 a wasan kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekaru 17, a birnin Yamai na Nijar.

wasan da aka kammala da yammacin Laraba ya ba Najeriya damar ci gaba da kasancewa ta daya a rukuninta na farko , Group A, da maki hudu da kwallaye uku.

Ita kuwa Guinea tana bin Najeriyar ne a matsayi na biyu ita ma da maki hudu amma da yawan kwallaye biyu.

Har wayau dai a rukunin na daya a daren Laraban nan ake fafatawa tsakanin Zambia ta uku da Nijar mai masaukin baki ta hudu.

Kasashe hudu da suka kai wasan kusa da karshe a gasar za su wakilici Afrika a gasar duniya da za a yi a Chile.

Za a yi gasar ta duniya ne tsakanin 17 ga watan Oktoba zuwa takwas ga Nuwamba na wanann shekara ta 2015, inda kasashe 24 za su fafata.