Ohuruogu ta soki shugaban IAAF

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption ''Bai dace ka yi wadannan kalamai ba tun da nauyin gyara a kanka yake''

'Yar tseren Birtaniya Christine Ohuruogu mai lambar zinare ta Olympics ta soki shugaban hukumar wasannin guje-guje ta duniya kan batun shan kwayoyin kara kuzari.

'Yar tseren ta Birtaniya ta soki Lamine Diack dan Senegal kan maganar da ya yi cewa wasan na fuskantar matsala saboda shan kwayoyin kara kuzari.

Shugaban a wata hira da BBC, ya ce ya kadu tare da damuwa kan zargin cewa jami'an wasan Rasha na da hannu wajen rufa-rufa kan shan kwayoyi da 'yan wasan kasar ke yi.

Ohuruogu ta ce, ''abu ne mai wuyar gaske a iya ciyar da wasanmu gaba idan bai san abin da ke wakana ba.Ta ce to aikin wane ne ?''

Ita ma dai Ohunurougu an taba dakatar da ita shekara daya saboda amfani da kwayoyin kara kuzari kafin ta dawo ta ci lambar zinariya ta duniya.

Ta kuma ci lambar zinariya ta Olympics a tseren mita 400 a 2008 a Beijin.

Haka kuma ta kasance 'yar tseren Birtaniya ta farko da ta ci lambobin duniya biyu, a lokacin da ta ci lambar zinariya a Moscow a 2013 , bayan wadda ta ci a 2007.