Fanareti: Rooney ya nemi gafara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Preston ma ya goyi bayan alkalin wasa

Golan kungiyar Preston Thorsten Stuckmann ya ce Wayne Rooney, ya nemi gafara kan yad da ya samu fanareti a lokacin wasansu na kofin FA ranar Litinin.

Rooney ya yi tsalle ne ya fadi a lokacin da golan ya tunkaro shi suka yi gaba da gaba, alkalin wasa ya ga kamar golan ya taba shi.

Mai tsaron gidan ya ce, ''Rooney ya ce min, yi hakuri damata ce ta samun fanareti. Dole na yi amfani da ita''

Stuckmann, ya ce idan da dan wasansu ne ya yi haka ya san alkalin wasa ba zai ba su fanareti ba.

Dan wasan na Ingila ya ci fanaretin ne wadda ta zama kwallo ta uku da ta bai wa Man United damar zuwa matakin wasan dab da na kusa da karshe da Arsenal.

Lamarin dai ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu sharhin kwallon kafa na BBC.

Hatta kociyan Ingila Roy Hodgson da Phil Neville da suka taba yin kungiya daya da Rooney sun goyi bayan Rooney.

Sun ce dole ne ya yi haka domin ya kaucewa golan wanda ya tunkaro shi gadan-gadan.

To amma tsohon dan wasan Jamhuriyar Ireland Kevin Kilbane, ya kafe cewa Rooney da gangan ya fadi,