Terry na son sabunta kwantaraginsa a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Terry ya kwashe shekaru goma sha shida yana taka leda a Chelsea

Kyaftin din Chelsea, John Terry, yana son tsawaita kwantaraginsa da watanni 12 a kulob din.

Dan wasan, mai shekaru 34, wanda kuma kwantaraginsa zai kare a kakar wasa ta bana, ya buga wa kulob din kwallo sau 650 a cikin shekaru goma sha shida.

Terry ya ce, "Kulob din [Chelsea] ya san matsayina; ina son zama a cikinsa. Ina sa rai za a bar ni na ci gaba da taka leda. Zan yi farin ciki idan na samu karin shekara daya. Ba ni da zabi."

Terry ya fara taka leda a Chelsea ne a shekarar 1998, kuma ya maye gurbin Marcel Desailly a matsayin kyaftin a farkon kakar wasa ta shekarar 2004-05.