Lallana na dari-dari

Hakkin mallakar hoto Liverpool
Image caption Lallana ya ce, ina fata magoya bayan Southampton za su yaba da lokacin da nake kungiyar

Dan wasan Liverpool Adam Lallana ya ce yana sa ran gamuwa da martani iri daban-daban lokacin wasansu da Southampton ranar Lahadi.

Wannan shi ne karon farko da Lallana zai je St Mary, gidan Southampton, tun bayan da ya bar kungiyar ya koma Anfield a watan Yuli.

Tsohon kyaftin din na Southampton, mai shekara 26, ya musanta rahotannin da ke cewa, ya bai wa kungiyar wa'adin su dauki wani mataki don hana tafiyar tasa.

Dan wasan na Ingila, ya ce ya san magoya bayan kungiyar ba su ji dadin tafiyarsa ba, amma dai bai ji dadin yanayin yadda ya bar kulab din ba.

Dan wasan ya ce bai taba furta cewa ba zai sake buga wa Southampton wasa ba.

Amma ya ce lokacin da Liverpool ta nuna sha'awarsa ya nemi Southampton ta tattauna domin barin sa ya tafi.