Dambe:Murray ya ce ya shirya wa Golovkin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Na zaku in yi ido biyu da Golovkin inji Murray na hannun hagu

Dan damben boksin na Birtaniya Martin Murray ya ce zai nuna rashin imaninsa a dambensa da Gennady Golovkin ranar Asabar.

Karawar ta kambun hukumar dambe ta duniya, WBA na matsakaita nauyi, da za a yi a Monte Carlo, ita ce ta uku ta kambun duniya da Murray ya taba nema.

Abokin karawar tasa dan kasar Kazakhstan, Golovkin mai shekara 32, a dambensa na ajin kwararru 31 ba a buge shi ba.

Kuma a wannan adadi ya yi wa abokan damben nasa 28 dukan kwabdaya. Ya dauki lamar azurfa a wasan Olympics na 2004, kuma a 2010 ya yi nasarar cin kambun WBA.

Murray mai shekara 32 ya ce, ''idan lokacin karawar ya zo zan fatattaka shi, na san gwani ne, amma zan nuna masa gwaninta ta.''

Murray wanda ya yi dambe 31 na kwararru, ya yi nasara a 29 da dukan kwab daya a 12, kuma an doke shi sau daya