Wariya: A hukunta magoya bayan Chelsea

Hakkin mallakar hoto
Image caption Magoya bayan na Chelsea sun hana mutumin shiga jirgin saboda wariyar launin fata

Mutumin da wasu magoya bayan kungiyar Chelsea suka hana shiga jirgin kasa kuma suke wakokin wariyar launin fata ya nemi da a hukunta su.

Mutumin mai shekara 33, Souleymane S, a wata hira da Le Parisien ta Faransa, ya ce, kamata ya yi a kulle magoya bayan na Chelsea.

A hirar da ya yi da jaridar Souleymane, ya ce abin bai ba shi mamaki ba, saboda yana rayuwa ne a cikin wariyar launin fata.

Mutumin wanda dan Faransa ne dan asalin kasar Mauritania, haifaffen Paris ya ce bai fahimci abin da mutanen ke cewa ba a lokacin, amma dai ya ce yasan ana nuna masa wariya ne ta launin fata.

Wani hoton bidiyo da aka nuna an ga yana kokarin shiga jirgin kasa, amma ana turo shi waje, ana kuma jin wasu na cewa mu masu wariyar launin fata ne kuma muna alfahari da haka.

Lamarin dai ya faru ne a wata tashar jirgin kasa ta Richelieu-Drouot da ke Paris babban birnin Faransa kafin wasan Chelsea da PSG na kofin Zakarun Turai na ranar Talata.

Hukumar 'yan sanda ta London ta ce ta dauki lamarin da muhimmanci kuma za ta taimaka wa hukumomin Faransa wajen gano mutanen a hukunta su.

Ita ma kungiyar Chelsea ta ce za ta taimaka wa 'yan sanda kan lamarin kuma za ta haramta wa duk wanda aka samu cikin lamarin mu'amulla da kungiyar.