Chelsea: 'Yan sanda sun gano masu wariya

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan sandan birnin London sun ce sun kaddamar da binciken ne domin tallafa wa 'yan sandan Faransa

Hukumar 'yan sandan birnin London ta ce ta gano mutane uku magoya bayan Chelsea da ake nema kan zargin laifin wariyar launin fata a jirgin kasa a Paris.

A ranar Juma'a aka bayyana hotunan mutanen uku da na'urar daukan hoto ta tsaro ta dauka lokacin da aka aikata laifin kafin wasan Kofin Zakarun Turai na PSG da Chelsea da suka tashi 1-1.

Hukumar 'yan sandan birnin London din ta ce ta kaddamar da binciken ne domin tallafa wa 'yan sandan Faransa.

Kungiyar Chelsea ta haramta wa magoya bayanta biyar zuwa Stamford Bridge har abada, sakamakon hoton bidiyon da aka nuna mutanen suna turo wani bakar fata daga jirgin kasa a Paris, sun hana shi shiga.

Kuma gungun mutanen na cewa su masu wariyar launin fata ne kuma suna alfahari da hakan.

Mai magana da yawun kungiyar ta Chelsea, ya ce klub din zai rubuta wasika ga mutumin da aka ci zarafin ya nemi gafararsa.

Shi kuwa kocin kungiyar Jose Mourinho cewa ya yi abin ya ba shi kunya da takaici.

Haka kuma hukumar 'yan sandan ababan hawa na Birtaniya, tana gudanar da bincike kan zargin rera wakokin wariyar launin fata da aka ce wasu magoya bayan Chelsea sun yi a tashar St Pancras da ke London da suke dawo wa daga wasansu a Paris.