Wariyar launin fata: Ferdinad ya yi gargadi

Image caption ''Ni kaina na yi sakaci akan yaki da matsalar''

Dan wasan baya na QPR, Rio Ferdinand ya ce yadda magoya bayan Chelsea suka ci zarafin wani bakar fata a jirgin kasa, ya nuna dole harkar kwallon kafa ta tashi tsaye don yaki da wariyar launin fata.

Kungiyar ta Chelsea ta haramta wa magoya bayanta biyar mu'amulla da ita akan lamarin da ya faru a Paris.

Tsohon kyaftin din na Ingila ya sheda wa jaridar The Sun ta Ingila cewa, ''mun fara tunanin cewa wasan kwallon kafa ya magance matsalar, har mun kawar da kanmu a kanta, amma kuma yanzu abin takaici ta kara tasowa.''

Ferdinand wanda dan kwamitin shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila Greg Dyke ne kan bunkasa harkar kwallon kafa, ya ce yanzu dole ne a cigaba da kokarin kawar da matsalar a kai a kai.

Dan wasan yana ganin dole ne hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa da ta duniya, Fifa, su kara tashi tsaye don magance matsalar ta wariyar launin fata.

Shi kuwa dan kwamitin amintattu na kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafa na Ingila Brendon Batson ya yi kira ne da a tuhumi magoya bayan Chelsean da laifin kai hari kan bakar fatar da suka ci zarafin.