Pellegrini : Man City za ta farma Barca

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A bara mun yi wasa 18 kafin mu hadu da su, bana mun fi su shiri

Kociyan Manchester City Manuel Pellegrini ya ce kungiyarsa ba za ta saurara wajen kai farmaki kan Barcelona ba a karawarsu ta farko ta kofin Zakarun Turai zagayen 'yan 16 ranar Talata a Etihad.

Kociyan ya ce za su yi wa Barca kamar yadda suka yi wa Newcastle ranar Asabar suka lallasa ta 5-0 a gasar Premier.

A karawar ta Manchester City da Newcastle, cikin minti 21 na farko zakarun na Premier suka zura kwallaye uku.

Pellegrini, ya ce a haduwar tasu da zarar an fara wasa za su rika kai hari ba kakkautawa domin su ci.

A bara Man City ta sha kashi da ci hudu da daya wasa gida da waje a hannun Barcelona a matakin 'yan 16, na sili daya kwale.

A karawar farko da aka yi a Etihad a shekarar da ta wuce din Barcelona ta doke Manchester City 2-0.

Nasarar ta Barcelona a kan City a bara, ta kai su wasan dab da na kusa da karshe karo na bakwai a jere, da yasa hakan suka tarar da Manchester United da Real Madrid.

A ranar Asabar Barcelona ta rasa damar zama ta daya a teburin La Liga bayan da ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a gidanta, a hannun tsohuwar kungiyar Pellegrini Malaga.